6 Maris 2021 - 08:17
Gwamnatin Biden Ba Ta Da Kyakyawar Niyyar Dage Wa Iran Takunkumi_Ruhani

Shugaba Hassan Ruhani, na Iran, ya bayyana cewa sabuwar gwamnatin Amurka, ba ta da kyakyawar niyyar dage wa Iran takunkumi.

ABNA24 : Iran, ta bakin shugaba Ruhanin ta ce, babatu da kuma rashin niyya ba zai warware takkadamar da ake ciki ba, dole sai an dauki matakai a aikace.

Ya kare da cewa idan dai har AMurka ta dage wa Iran, takunkumi, to ita ma Iran, za ta dakatar da matakan da take dauka game da yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da ita.

Shugaba Ruhanin wanda ke bayyana hakan a taron mambobin gwamnatinsa, ya kara da cewa abu ne mai sauki dagewa Iran, takunkumi idan dai har gwamnatin ta Amurka tana da niyyar yin hakan.

342/